18 Maris 2026 - 15:52
Source: ABNA24
Iran Ta Kai Hari Kan Dukkan Sansanonin Amurka A Yankin Da Wuraren Taruwar Sojojin Sahyoniyawa

 Ofishin hulda da jama’a na IRGC: Cikin jerin ayyukan hare-haren kashi na 62 cikin tsananin karfi cikin 'yan sa'o'i dakarun Iran sun kai hari kan wuraren abokan gaba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: IRGC cikin jerin ayyukan mai da martani kasha na 62 a sa’o’in da suka gabata sun kai hari da ramznin sunan: (Ya Aliyu Bin Musar Ridha As) kan dukkan sansanonin Amurka da ke yankin da wuraren taruwar cibiyoyin soja da na sahyoniya da makamai masu linzami na Qadr-dake dauke da kawunan bama-bamai masu yawa- da makamain Khaibar Shikan da Emad da makamin Hajj Qasem. Inda ta sdauakar da wannan haring a shahidan da ake gudanar da jana’izarsu yanzu wanda suka hada da shahidan jirgin Dena da jinin Dakta Ali Larijani da Manjo Janar Gholamreza Soleimani.

Wuraren da akai kaiwa harin sun hada da Cibiyoyi a Acca, Haifa, Tel Aviv, da Beersaba bayan lalata na’urorin tsaro masu ci gaba na gwamnatin Sahayoniya da na Amurka na mai aikata ta’addanci, wanda hara-haren sun sauka ba tare da kunnuwar ƙararrawa gargadi ba.

Hakanan hare-haren sun isa ga Duk sansanonin Amurka a yankin a karo na uku a jere da ke Alis -Salam, da Victoria, da Al-Kharaj, Al-udaid, da Al-udairi, da Al-Zafarah, da Al-Azraq, da jirgin yakin ruwa Navy na Biyar da ke Uraifajan an kai hari da makamai masu linzami masu ƙarfi masu dauke da kawukan bam dayawa da jiragen yaki marsa matuki masu inganci da yawa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha